Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya habarta maku cewa: Mutane 28 ne suka mutu sakamakon kifewar motar ziyarar Arba'in ta Pakistan a Yazd, 14 sun samu munanan raunuka.
Adadin wadanda suka mutu da jikkata a lokacin da motar bas din maziyartan Pakistan ta kife a gundumar Dehshir Taft ya kai 28. Babban daraktan kula da tabarbarewar yanayi na lardin Yazd ya bayyana cewa: Adadin wadanda suka mutu da kuma jikkata sakamakon kifawar da wata motar bas din maziyartan Pakistan a gundumar Dehshir Taft ya kai 28.
"Muhammed Ali Malekzadeh" ya kara da cewa a safiyar Larabar nan: "An ba da rahoton cewa, yanayin 14 daga cikin wadanda suka jikkata da aka kwantar a cibiyoyin kiwon lafiya na Shahid Rahmonun, Abarkoh da Taft yayi matuƙar munana".
Ya sanar da lokacin faruwar wannan mummunan lamari da misalin karfe 21:54 na daren ranar Talata kuma adadin fasinjojin da ke cikin motar wadanda dukkansu ‘yan kasar Pakistan ne kuma suke tafiya daga wannan kasar Iran zuwa kasar Iraki domin gudanar da ziyara da taron Arbain, ya mutane 51.
Malekzadeh ya bayyana cewa: Gwamnatin Yazd tare da hadin gwiwar ma'aikatar harkokin wajen kasar ta dauki matakin ware wani jirgin sama domin jigilar wadanda suka jikkata da wadanda suka mutu a wannan hatsarin zuwa Pakistan.
Ya ci gaba da cewa: An kai wadanda suka mutun zuwa asibitin kwararru domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar, kuma likitoci 9 na gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ‘yan sanda suka tattara kayan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.
A cewarsa, masu aikin ceto na ci gaba da binciken lamarin har zuwa karfe uku na safe.
.................................